Halin da muke ciki a Nijar – Yusuf Buzu

0
259

Hankula sun karkata game da matakan da Kungiyar Bunkasa Tattalin Arzikin Yammacin Afirka (ECOWAS) ke ci gaba da dauka domin mayar da martani a kan juyin mulkin da sojoji suka yi a Nijar, a kwanan nan takunkuman da aka kakaba wa kasar sun zama ababen tattaunawa a Tsakanin ‘Yan Nijeriya da Nijar. LEADERSHIP Hausa ta tattauna da wani Dan Nijar, YUSUF HACHIMOU da ke Birnin Tawa, domin jin halin da suke ciki yayin da takunkuman da aka kakaba wa kasar suka fara aiki.

Ga yadda ta kaya:

Da farko mene ne cikakken sunanka da inda kake a yanzu haka a Nijar?

Assalamu alaikum. Sunana Yusufa Hachimou amma, inkiyata kuma Yusufa Buzu. Sannan an haife ni a cikin garin Tawa Anguwar Nasarawa bakin Silema, shekaruna yanzu haka kuma 33 a duniya. Ina godiya fa Allah shi sa mu dace, shi zaunar da Kasarmu Nijar da Nijerya lafiya. Dukkan abin da ke wargaza Nijar da Nijeriya Allah shi yi muna maganin sa, don isar Annabi da alkur’anni.

Wane hali ake ciki a Nijar sakamakon takunkuman da ECOWAS ta kakaba wa kasar, ko akwai wani matsi da ‘yan kasar suka fara shiga?

Wallahi Nijar muna cikin kuncin rayuwa, domin kamin a yi juyin mulki muna sayen abinci kamar shinkafa a kan jika goma shadaya da rabi, sai gamu yanzu shinkafa ta koma jika sha biyar, mai na abinci a baya dari da tamanin ne yanzu kuma jika da hamsin. Ka ga kuwa dole ne talaka shi sha wahala, fatanmu Allah shi kawo muna sauki a cikin kasarmu Nijar da Nijeriya baki daya don isar Annabin rahama (SAW). Abin mamaki su dai ‘yan kasuwa me ya sa suke yin haka? kayansu akwai, su ba wasu aka shigo da su balle su ce an samu karin farashi.

Wannan gaskiya shi ne babban ibtila’i ga talaka, a nan Tawa akwai kauyuka da yawa da ‘yan ta’adda sun hana zama abin kawai sai addu’a, don haka mu dai a wajen mu da mulkin soja da na farar hulla a wajen talaka dukkansu daya ne. Sannan shawarata ga ‘yan kasuwa su ji tsoron Allah su daina yin karin kudi a kan abinda muke yin mu’amalla yau da kullum.

Haka nan, ina kira da babbar murya ga Nijar da Nijeriya da mu ci gaba da zama a matsayin uwa daya uba daya, kada mu sa wa kanmu gabba da juna, ka san daga cikin mutane akwai masu ganin Nijar yunwa gare ta ko masu wulakanta dan Nijar kamar shi ba kowa ba ne. Mu sani cewa Nijar da Nijeriya al’adunmu daya, addininmu guda da sutturanmu duka daya ne. Don haka, me ya sa ake son hada mu rigima da juna? Allah shi kara hada kawunanmu baki daya, sannan dukkan makiyan Kasarmu Nijar da Nijeriya na fili da na boye, ya Allah shi wargaza su, shi kuma yi muna jagora ga dukkan lamuranmu na alheri don isar Annabin rahama (SAW).

Mun ga masu Zanga-zangar goyon bayan sojoji sun fito gangami, ko wannan yana nuna masu goyon bayan abin sun fi wadanda ba su goyon baya yawa, ina ne talakawa ‘Yan Nijar suka fi raja’a?

Ka san shi talaka bai san inda yake yi mai ciwo ba wallahi, wanda yake yin murna bai san juyin mulki ba ne, talakawa sun fi yawa ga goyon bayan soja. Ka san me ya kawo hakan? An gajji da mulkin jam’iyyar PNDS Tarayya ne, komai in lokacinka ya zo karshe tau ka hakora zuwa gaba ka sake fitowa kuma mu ‘yan Nijar muna son Bazom da tsohon Shugaban Kasarmu Nijar Isoupou Muhammadu, damuwar kabilar Nijar wato Zabarmawa sun fi mu murnar juyin mulki. Duk da dai akwai Hausawa amma fa Zabarmawan tuni sun gaji da mulkin Jam’iyyar PNDS Tarayya, ga shi Allah ya kawo karshen mulkin nasu don haka a rungumi kaddara ba tayar da hankali ba. Allah shi kawo muna karshen wanan musiba da bala’i a cikin Kasarmu Nijar da Nijeriya don hasken fuskar Manzon Allah SAW.

Ta yaya yanke lantarkin da Nijeriya ta yi wa kasar ke shafar rayuwar mutane?

Gaskiya wannan yanke wutar lantarki ya harzuka ‘yan Nijar, a nan kowa ya yi tofin Allah tsine, babu wani zaman sulhu da wasu manyan Shugabannin Nijar kwatsam sai Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya ce ya cire wuta. Ka ga a nan an yi babban kuskure, sai ga shi allura ta tono galma ashe akwai yarjejeniyar da aka yi tsakanin Nijar da Nijeriya. Haka zalika ka ga yanzu an rufe bodarmu da Nijeriya, yanzu haka mu da Nijeriyar ba a san wanda ya fi shan wahala da shiga tashin hankali ba. Kirana ga ‘yan Nijar a nan shi ne, mu dage da yi ma Kasarmu Nijar da Nijeriya addu’a Allah shi zaunar da mu lafiya don isar Annabi da Alkur’ani.

Ta yaya yanke lantarkin da Nijeriya ta yi wa kasar ke shafar rayuwar mutane?

Gaskiya wannan yanke wutar lantarki ya harzuka ‘yan Nijar, a nan kowa ya yi tofin Allah tsine, babu wani zaman sulhu da wasu manyan Shugabannin Nijar kwatsam sai Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya ce ya cire wuta. Ka ga a nan an yi babban kuskure, sai ga shi allura ta tono galma ashe akwai yarjejeniyar da aka yi tsakanin Nijar da Nijeriya. Haka zalika ka ga yanzu an rufe bodarmu da Nijeriya, yanzu haka mu da Nijeriyar ba a san wanda ya fi shan wahala da shiga tashin hankali ba. Kirana ga ‘yan Nijar a nan shi ne, mu dage da yi ma Kasarmu Nijar da Nijeriya addu’a Allah shi zaunar da mu lafiya don isar Annabi da Alkur’ani.

Mene ne ra’ayoyin ‘yan kasa game da barazanar matakin soja ta ECOWAS?

Gaskiya dukkan dan Nijar ya yi bakin ciki da jin wai Nijeriya ce kan gaba wajen yakar Nijar, in ban da shigowar Malaman Nijeriya ciki da suka yi da sauri da yanzu an tafka asara. Da yake mu mutanen Nijar mun gane cewa Shugaban Kasar Nijeriya Tinibu, ba dan Arewa ba ne da dan Arewa ne ba zai taba yin wannan furuci ba, don kuwa in sha Allahu sai ka ji Kaka nai wajen uwa ko uba daga Nijar ne, don mu ‘yan Nijar muna tare da Nijeriya kuma uwa ce gare mu. Abin da ya sa na fadi haka kuwa, don ni Yusufa Buzu mahaifina mutumin Sakkwato ne, a Karamar Hukumar Wamako cikin Kauyan Kwamna.

Mene ne ra’ayoyin ‘yan Nijar da ke kasashen waje game da wannan lamari?

Tau yanzu dai mutanen Nijar da ke kasashen waje sun goyi bayan soja kuma sun fi yawa gaskiya, tunda da ma babban abin da ke sawa barin kasar rashin aikin yi ne a gida. Tsawon shekara goma sha biyu ana mulkin demokaradiyya a kan Jam’iyyar PNDS Tarayya, amma mu ‘yan Nijar babu wani aikin yi a kasa, Kamfani ko guda babu wanda dan Nijar zai yi aiki. Wannan dalili ne ya sa dole a tafi bidar aiki a kasashen waje, da an yi mana wajen aiki a gida da yanzu mun rage fita kasashen na waje sai yanzu a aka yi mana wani Kafanin Siminti, shi ne ziyarar da Shugaban Kasar tamu ta Nijar Bazom ya zo ya bude, komawarsa ke da wuya aka yi masa juyin mulki.

Sannan gaskiya akwai alamun ci gaba a rayuwarshi, sai dai kash! iyya abin da zai yi ya yi sai dai mu hari nan gaba in da rai in sha Allah tenuwa mai zuwa idan za a yi zabe, Bazom zai iya ci da yardar Allahu. In dai har shina da sha’awar dawowa mu dai fatanmu shi ne, Allah shi kawo muna karshen wannan musiba da bala’i a cikin kasarmu Nijar da Nijeriya, Allah shi yi muna maganin azzaluman kasarmu, shi amsa muna ibadunmu baki daya don isar Annabi Muhammadu (SAW).

Ko zuwa yanzu malaman addini a Nijar sun yi magana kan abubuwan da suke faruwa, idan sun yi, ina ne hankulansu suka karkata?

Dangane da Malaman Nijar shi ne, wasu daga cikin Malaman Nijeriya su ne suka fara yin raddi ga masu juyin mulki. Ka san Hausawa na ce fadin cewa fadan da ba naka ba dadin kallo gare shi, ita dai gaskiya guda ce daga kin ta sai halaka. Domin kuwa har ma sun fara yin fada a cikin karatunsu daga baya kuma kowa ya gane abin da ya dace, don haka alhamdu lillahi ta kowane bangare addu’a a ake yi wannan damuwa ta wuce domin kuwa sharrin shedani ne, sannan komai shina da lokaci kuma shina da sanadi dukkan bala’i a cikin kowane yanayi za ka ji an ce a nemo malamai su yi addu’a. Allah shi kara zaunar da kasarmu Nijar da Nijeriya lafiya don isar Annabin rahama (SAW), yanzu a halin da muke ciki a Nijar kura ta lafa in sha Allahu ko a can Birnin Tarayya Yamai, kowa shina harkokinsa cikin lumana in sha Allahu. Allah shi sa mu dace shi kuma sa hakan shi ne alheri ga Kasarmu Nijar da Nijeriya.

Maganata ta karshe zuwa ga sabon Shugaban Kasarmu Nijar Janaral Abdourahamane Tchiani, shi sani akwai babban aiki a gabansa na hada kan ‘yan Nijar. Saboda haka, muna yi masa addu’a Allah shi taya shi riko, shi yi mai kariya gaba da bayansa. Dukkan abin da zai ayyana a Kasarmu Nijar, Allah shi sama sa hannu shi kuma dauka cewa babu siyasa yanzu aiki kawai aka zo yi.

Haka zalika, dukkan masu ba shi shawara a kan wanan tafiya Allah shi yi mai zabin su nagari masu kishin kasa, ba aljihunsu ba. ‘Yan uwana musulmi mutanen Nijar da Nijeriya, dukkan mu mu sani cewa tare muke ka da wanan sha’ani shi sa mu rika yi ma junna kallon hadarin kajji. Allah shi zaunar da kasarmu Nijar da Nijeriya lafiya don isar Annabi da alkur’ani, dukkan masu ganin mun shiga rigima da junanmu, ya Allah ka wargaza shirinsu a kan kasashenmu na musulunci don tsarkin mulkinka. Allah mun tuba ka yafe muna kurakuranmu na fili da na boye don isar Annabin rahama (SAW), idan mutuwarmu ta zo ka sa mu cika da kalmar shahada alfarmar Manzon Allah (SAW).

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here