ECOWAS ta bai wa rundunarta umarnin karbo mulki a Nijar

0
104

Kungiyar Kasashen Yammacin Afrika ta ECOWAS ta umarci rundunarta da ke cikin shirin-ko-ta-kwana da ta maido da kundin tsarin mulki a Jamhuriyar Nijar.

Shugaban gudanarwar ECOWAS Omar Alie Touray ya bayyana haka a lokacin da yake karanta kudirorin da kungiyar ta dauka game da juyin mulkin Nijar a wani taro da ya gudana birnin Abuja na Najeriya a wannan Alhamis.

ECOWAS ta bayyana cewa, ta dauki matsayar ne bayan ta nazarci rahoto da kuma shawarwarin da Kwamitin Hafsosshin Tsaronta suka bayar, tana mai korafin cewa, daukacin hanyoyin diflomasiyar da ta bi don warware rikicin siyasar kasar sun ci-tura sakamakon yadda sojojin suka yi juyin mulki suka ki mutunta umarnin da aka ba su.

ECOWAS ta bai wa sojojin na Nijar wa’adin ranar 6 ga wannan wata na Agusta da su mayar da shugaba Mohamed Bazoum kan kujerarsa ta shugaban kasa, amma suka ki mutunta wannan umarni.

Yanzu haka ECOWAS ta jaddada matsayarta na yin Allah-wadai da juyin mulkin gami da ci gaba da tsare shugaba Bazoum da iyalansa da wasu jami’an gwamnatinsa.

Kungiyar ta kasashen yammacin Afrika ta sanar da tsaurara matakan rufe kan iyakokin Nijar da haramta tafiye-tafiye da daskarar da kadarorin wadanda ke da hannu a juyin mulkin bayan ta gaza magance rikicin kasar ta hanyar laluma.

A bangare guda, ECOWAS ta bukaci Kungiyar AU da ta amince da daukacin kudirorin da ta dauka a dalilin halin da ake ciki a Jamhuriyar Nijar.

Har ila yau, ECOWAS ta yi kira ga kasashen duniya aminanta da Majalisar Dinkin Duniya da su mara mata baya domin samun natija ta gaggawa dangane da maido da kundin tsarin mulki a Nijar.

Kawo yanzu dai, sojojin da suka yi juyin mulkin na Nijar ba su nuna wata alamar shiga tattaunawar fahimtar juna da ECOWAS ba duk kuwa da tarin takunkuman da aka malkaya musu baya ga barazanar daukar matakin sojin da aka yi musu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here