Kotu ta soke zaben dan majalisar wakilai a Kano

0
310

Kotun sauraron ƙorafin zaɓe da ke zama a Kano ta soke zaɓen Honourable Muktar Umar Yarima mai wakiltar Tarauni a majalisar wakilai saboda amfani da takardu shaidar kammala karatu na bogi.

A hukuncin da alƙalan kotun uku suka bayar, sun ce sun samu Yarima da gabatar da takardar kammala karatun firamare na bogi, don haka kotun ta umarci hukumar zabe ta ƙasa ta ayyana ɗan takarar jam’iyyar APC, Honourable Hafizu Ibrahim Kawu a matsayin wanda ya lashe zaɓen.

A baya dai jami’in sanar da sakamakon zaben zamaɓar Tarauni, a zaɓen da ya gabata, Garba Galadanci ya sanar da Yarima na jam’iyyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben, bayan samun ƙuri’a 26,273, ya kuma doke Honourable Hafizu Ibrahim Kawu na jam’iyyar APC wanda ya samu ƙuri’a 15,931.

Daga baya Kawu ya shigar da ƙara, inda ya ƙalubalanci sakamakon zaɓen a bisa zargin gabatar da takardun bogi daga ɓangaren wanda ya yi nasarar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here