Shin ECOWAS ta janye barazanar da ta yi wa Nijar?

0
174

Kungiyar Kasashen Afrika ta Yamma, wato ECOWAS, ta ce za ta ci gaba tintibar sojojin da suka yi juyin mulki a Jamhuriyar Nijar a yunkurin da take na warware matsalar, a wani yanayi da ke nuna alamun janye barazanar amfani da karfin soji domin mayar da zababiyar gwamnatin kasar.

Yayin bude taro na musammman da shugabannin kungiyar  a Abuja, shugaban ECOWAS Bola Ahmed Tinubu da ke jagorancin taron ya bayyana taron na yau a matsayin mai matukar muhimmanci wajen ci gaba da dorewar yankin a matsayin dunkulalliya wadda za ta taimaka wajen tabbatar da zaman lafiya da kuma ci gaban jama’arta. 

Shugaban ya ce taronsu na yau zai bada damar cikakken nazari kan ci gaban da aka samu da kuma matsalolin da aka fuskanta tun bayan taron farko da suka yi kan Nijar, domin duba gyaran da ya kamata a yi ko kuma gibin da ya kamata a cike domin gyara lamarin. 

Tinubu ya ce a matsayinsu na masu kare demokiradiya, ya zama wajibi su tintibe kowanne bangare, cikinsu har da da sojojin da suka yi juyin mulki domin ganin sun amince da bukatar mayar da zababben shugaban kasa Bazoum Mohammed karagar mulki. 

Shugaban na ECOWAS ya ce ya zama wajibi a gare su a matsayin shugabanni su fahimci cewar halin da ake ciki a Nijar na zama barazana a gare su, kuma abin da ke iya biyo baya zai shafi yankin baki daya. 

Tinubu ya bayyana fatar cewar wannan taro na biyu kan Nijar zai bada damar daukar matakin da ya dace wanda zai taimaka wa yankin baki daya. 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here