Kungiyar Shi’a a Najeriya sunyi adawa da amfani da karfin soji a Nijar

0
191
Yan Shi'a
Yan Shi'a

Kungiyar ta Shi’a ta bayyana matsayarta ne yayin da shugabannin kasashen kungiyar ta ECOWAS ke taro a Abuja don duba mataki na gaba da za su dauka.

Kungiyar mabiya akidar Shia’a a Najeriya ta bi sahun wasu kungiyoyi da daidaikun jama’a wajen nuna adawa da amfani da karfin soji a Nijar.

Har yanzu dai ana jiran tsammani abin da zai iya faruwa a takaddamar da ke tsakanin sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar da kuma Kungiyar ECOWAS, da yake wannan Alhamis ce kungiyar ta ECOWAS ke batun daukar mataki na gaba, bayan karewar wa’adin farko da ta bayar a mayar da mulki ga farar hula da aka hanbarar.

Sai dai har yanzu alamu na nuna jama’a daga Najeriya wadda Shugabanta ne ke jagorancin Kungiyar ECOWAS har ma da mutanen Nijar da wasu kasashe suna adawa da yin amfani da karfin soji wajen kawar da sojojin da suka yi juyin mulkin.

Wakilai na kungiyar mabiya akidar Shi’a, a Najeriya sun hadu a Jihar Sakkwato da ke Arewa maso Yammacin Najeriya, suka nuna adawa da daukar matakin soji a Nijar.

Jagoran masu nuna adawar Mainasara Ibrahim Sokoto ya ce suna nuna kin amincewar da kai yaki Nijar ne saboda Nijar da Najeriya tamkar Hassan da Hussain ne kuma idan har aka fara yakin, daga karshe a kan talaka ne masifar zata kare.

Mabiya akidar ta Shi’a ta ce tana mamaki duk da matsalar tattalin arziki da kasashen Afirka ke fuskantar, ECOWAS na yunkurin halaka makudan kudade wajen yakar Nijar.

Ko a can baya wasu kungiyoyi da daidaikun jama’a sun yi ta nuna adawa da matakin da ECOWAS ta ce za ta dauka na amfani da Soji a kasar Nijar, abinda suke cewa ba shi ne mafita ba.

Yanzu dai matakin na gaba na kungiyar ta ECOWAS shi zai nuna ko ta saurara tare da karba kiraye-kirayen jama’a ko akasin haka.

Tuni dai jami’an Sojin na kungiyar ECOWAS suka ce suna cikin shirin ko-ta-kwana domin zartar da umurnin da kungiyar za ta bayar, yayin da su kuma jami’an Gwamnatin Soji na Jamhuriyar Nijar suka himmantu wajen sha’anin tafiyar da mulkin kasar, abinda ke nuna basu da niyar karba bukatar ta ECOWAS.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here