Ƙungiyar tawaye da juyin mulkin sojoji ta ɓulla a Nijar

0
249

Wani tsohon jagoran ‘yan tawaye kuma ɗan siyasa a Nijar ya ce ya kafa wata ƙungiya a ƙoƙarin mayar da hamɓararren Shugaba Mohamed Bazoum kan karagar mulki.

Rhissa Ag Boula ya ce ƙungiyar tasa mai suna Majalisar Nuna Bijirewa don Tabbatar da Jamhuriya) za ta tallafa wa ƙoƙarin dawo da gwamnati mai aiki da tsarin mulki a Nijar.Wannan ita ce alama ta farko mai nuna ɓullar gwagwarmayar nuna turjiya ga juyin mulkin da sojoji a cikin gida.An jiyo Mallam Rhissa Ag Boula, jim kaɗan bayan juyin mulkin ranar 26 ga watan Yuli yana kira ga Ƙabilun Larabawa, Abzinawa da Toubawa su ɗauki makamai don mayar da Nijar kan tsarin dimokraɗiyya

Ƙungiyar Raya ƙasashen Afirka ta Yamma Ecowas wadda ta yi barazanar amfani da ƙarfin soja, za ta yi taro ranar Alhamis don tattaunawa a kan wannan dambarwa.Wata sanarwa da jagoran tawayen ya fitar na cewa “Nijar ta sha fama da tashin hankali daga mutanen da aka damƙa wa alhakin kare ta”.Bayyanar ƙungiyar ta zo ne daidai lokacin da ƙoƙarin diflomasiyya don warware juyin mulkin na sojoji ga alama ya tsaya cik.Shugabannin mulkin Nijar sun ƙi karɓar ayarin jami’an diflomasiyya na baya-bayan nan, kuma gwamnatocin soji a maƙwabtan ƙasashe kamar Mali da Burkina Faso, waɗanda ke mara baya ga juyin mulkin, sun yi kira ga Majalisar Ɗinkin Duniya ta hana duk wani amfani da ƙarfin soji a kan Nijar.Shugabannin juyin mulkin sun hana jami’an diflomasiyyar Tarayyar Afirka da na Majalisar Ɗinkin Duniya da kuma na ƙungiyar Ecowas shiga Nijar, a yunƙurinsu na bijire wa matsin lambar hawa teburin tattaunawa gabanin taron ƙolin da Ecowas za ta gudanar ranar Alhamis, inda ake sa ran za ta duba yiwuwar amfani da ƙarfin soji.

Ƙungiyar ‘yan tawayen CRR dai za ta mara baya ga Ecowas da kuma sauran masu ruwa da tsaki na ƙasashen duniya da neman dawo da gwamnati mai aiki da tsarin mulki a Nijar, a cewar sanarwar Ag Boula, wadda ta yi alƙwarin cewa za ta gabatar da kanta ga ƙungiyar Ecowas don yin amfani da ƙarfinta ta kowacce fuska.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ambato CRR na cewa ‘yan siyasar Nijar masu yawa sun shiga cikin ƙungiyar, amma ba za su bayyana matakin a bainar jama’a ba saboda dalilai na tsaron lafiya.

Sai dai tuni rukunin al’ummar Nijar daga ɓangarori daban-daban suka fara kira ga Rhissa Ag boula ya maida wuƙa kube domin samun wanzuwar zaman lafiya a ƙasar.

Wane ne Rhissa?

Rhissa Ag Boula ya ba da gagarumar gudunmawa a tashe-tashen hankulan shekarun 1990 da kuma shekarun 2000 na Azbinawa, ƙabila mai zama a wuri na wani ɗan lokaci kafin ta tashi, da aka fi samun ta a yankunan hamadar arewacin Nijar.

Kamar tsoffin ‘yan tawaye da dama, an shigar da shi cikin gwamnatin Bazoum da kuma ta magabacinsa Mahamadou Issoufou.

Ko da yake ba za a iya fayyace girman goyon bayan da CRR take da shi ba, amma sanarwar Ag Boula za ta janyo damuwa ga masu juyin mulkin Nijar bisa la’akari da tasirin da yake da shi a tsakanin Azbinawa.

Su ne dai ke iko da harkokin siyasa da kasuwanci a mafi yawan yankin arewacin Nijar

Blinken ya zanta da Bazoum

Sakatare Wajen Amurka Antony Blinken ya zanta da hamɓararren shugaban Nijar Mohamed Bazoum a kan ziyarar da jami’ar diflomasiyyar Amurka Victoria Nuland ta kai Nijar.

Ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta ce “mutanen biyu sun tattauna game da ziyarar da Mataimakiyar Sakataren Wajen ta riƙo, ta kai birnin Niamey kuma sakataren ya bayyana ci gaba da goyon bayan Amurka da nufin lalubo wata hanya da za a mayar da Nijar kan mulkin dimokraɗiyya da kuma gwamnati mai aiki da tsarin mulkin ƙasa”.

“Sakataren ya kuma nanata cewa tsaron lafiya da na rayuwar Shugaba Bazoum da iyalinsa, na da matuƙar muhimmanci.”

Tun bayan juyin mulkin ranar 26 ga watan Yuli ne, sojoji suke tsare da Shugaba Bazoum a gidansa da ke birnin Yamai.

Victoria Nuland ta faɗa a ranar Litinin cewa ta kai ziyara Yamai babban birnin Nijar kuma ta gudanar da tattaunawa “mai wahala da tsage gaskiya da manyan jami’an sojin da suka yi juyin mulki.

A zantawa da manema labarai, Nuland ta ce shugabannin mulkin sojin ba su karɓi shawarwarin Amurka na su mayar da ƙasar kan tsarin dimokraɗiyya ba kuma sun ƙi ba ta damar ganawa da Bazoum.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here