Juyin Mulki: Bazoum ya bayyana halin da ya shiga a hannun sojojin Nijar 

0
241

Hambararren shugaban Jamhuriyar Nijar, Mohamed Bazoum, ya ce an killace shi tare da tilasta masa cin busasshiyar shinkafa.

Shugaba Bola Tinubu, wanda shi ne Shugaban Kungiyar bunkasa Tattalin Arzikin Yammacin Afirka (ECOWAS), ya shirya wani taro a yau Alhamis bayan wa’adin kwanaki 7 da kungiyar ta fitar na maido da Shugaba Mohamed Bazoum kan mukaminsa ya cika.

Tashar talabijin ta CNN ta ruwaito Bazoum a cikin jerin sakonnin tes da ya aike wa wani abokinsa yana cewa “an hana shi hulda da mutane” tun daga ranar Juma’a, ba tare da an kai masa abinci ko magunguna ba.

A cewar hambararren shugaban, ya shafe mako guda yana rayuwa a Ina babu hasken wutar lantarki, al’amarin da ya zama ruwan dare ga daukacin ‘yan Nijar bayan da Najeriya ta katse wutar lantarki sakamakon juyin mulkin.

Bazoum ya ce duk abincin da aka kawo masa ya lalace, kuma yanzu yana cin busasshiyar taliya da shinkafa.

Duk da keɓantace shi, Bazoum yana samun goyon bayan ƙasashen duniyar. Ko da yake an ki bashi damar tattaunawa da mataimakiyar sakatariyar harkokin wajen Amurka Victoria Nuland a ziyarar da ta kai Yamai babban birnin Nijar a ranar Litinin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here