Birtaniya ta sanya wa wasu takunkumi kan taimakawa Rasha

0
461

Birtaniya ta sanar da abin da ta kira mataki mafi girma da ta taba dauka a kan wata kasa da ba ta Turai ba, da ke sama wa Rasha makamai.

“Wadannan sabbin takunkumai an sa su ne da nufin takaita wa Rasha hanyar samun makamai Wadanda matakin ya shafa sun hada da wasu kamfanoni biyu na Turkiyya, da ake zargin suna sama wa Rasha kananan na’urorin laturoni.

Akwai kuma wani kamfanin da ke Dubai wanda shi kuma ake zarginsa da aika wa Rashar kananan jiragen sama marassa matuka, da kuma kayan jiragen.

Haka kuma Birtaniyar ta sanya takunkumi a kan wani dan kasar Slovak a kan hannun da yake da shi a wata yarjejeniyar makamai tsakanin Koriya ta Arewa da Rasha.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here