An kashe mutane da dama a harin da Rasha ta kai Gabashin Ukraine

0
179

Wani harin da Rasha ta kai garin Pokkrovsk da ke Gabashin Ukraine ya kashe mutane aƙalla biyar.

Ministan harkokin cikin gida, Ihor Klymenko ya ce harin ya kashe fararen hula huɗu da wani jami’in gwamnati, tare da raunata wasu mutum 31. 

Shugaba Volodymyr Zelensky ma ya ce an samu mutanen da suka mutu a harin, amma bai faɗi yawan su ba. 

Masu aikin ceto na ci gaba da neman zaƙulo waɗanda harin ya ritsa da su. 

Garin Pokrovsk yana da nisan kilomita 70 da Arewacin birnin Donetsk city, anda kuma dakarun Rasha suka mamaye. 

Kafin ɓarkewar yaƙin birnin yana da mutane aƙalla dubu 60.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here