Arsenal ta lashe kofin Community Shield a hannun Man City

0
182


Arsenal ta kara wa fatanta na doke Manchester City a gasar Premier League kwarin gwiwa bayan ta lashe Community Shield a wasan da ta doke kungiyar ta Pep Guardiola 4-1 a bugun fenariti.

An tashi wasan 1-1 ba tare da buga Æ™arin zagaye biyu na Æ™arin lokaci ba. 

Matashin dan wasan Mancherster City Cole Palmer ne ya fara jefa kwallo a ragar Arsenal a minti na 70, kafin Leandro Trossard ya farke ta a minti na 101 bayan ƙara minti 8.

A haka wasan ya kai zuwa bugun Fenariti, inda Kevin de Bruyne da Rodri suka zubar ma City, sannan Fabio Vieira ya jefa wa Arsenal bugun karshe da ya tabbatar da nasarar tata.

Yanzu kungoyin biyu za su saurari fara gasar Premier ta bana a mako mai zuwa, inda Man City za ta kara da Burnley ranar Juma’a, ita kuma Arsenal ta karbi bakuncin Nottingham Forest ranar Asabar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here