Sojojin Nijar na neman agajin dakarun Rasha

0
255

Sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar sun bukaci tallafin sojoji daga rundunar sojojin haya ta Wagner a daidai lokacin da wa’adin da kungiyar ECOWAS ta bayar na mika mulki ga farar hula ke kawo karshe.

Neman agajin na zuwa ne a lokacin da daya daga cikin jagororin juyin mulkin, Janar Salifou Mody ya je Mali mai makwaftaka, inda ya hadu da wani daga rundunar ta Wagner, Wassim Nasr, kamar yadda wani dan jarida kuma babban mai bincike a Cibiyar Soufan ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AP.

Ya bayyana cewa wasu majiyoyi uku daga Mali da kuma wani jami’in diflomasiyya na Faransa ya tabbatar da tattaunawar wadda gidan talabijin na France24 ya soma bayar da labari a kai.

“Suna bukatar (Wagner) saboda za su zama wani tabbaci a gare su na rike mulki,” in ji shi, inda suka kara da cewa rundunar na duba bukatar ta su.

Wa’adin ranar Lahadi

Wani jami’in soji na daya daga cikin kasashen Yamma wanda bai so a bayyana sunansa domin ba a amince ya yi magana ba, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AP cewa su ma sun ji labarin cewa sojojin na Nijar na neman taimako daga Wagner da ke Mali.

Zuwa ranar Lahadi ne wa’adin sojin Nijar din da kungiyar ECOWAS ta bayar ke karewa domin saki da kuma mayar da zababben shugaban kasar Mohamed Bazoum kan mukaminsa.

Shugabannin tsaro na kasashen ECOWAS sun cimma matsaya kan cewa amfani da karfin soji a ranar Juma’a inda suka bukaci sojojinsu da su zama cikin shiri bayan da aka tura masu shiga tsakani Nijar a ranar Alhamis inda aka ki barin su gana da shugaban kasar na mulkin soji Janar Abdourahmane Tchiani.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here