Pakistan: An yi arangama tsakanin ‘yan sanda da magoya bayan Imran Khan

0
144

An yi mummunar arrangama tsakanin jami’an tsaro da gungu gungu na masu zanga-zangar da suka fantsama kan titunan sassan Pakistan a wannan Talata, bayan da aka kama tsohon Firaministan kasar Imran Khan

‘Yan sanda sun kama Imran Khan ne, bayan da ya bayyana a gaban wata Kotu akan wasu jerin tuhume-tuhume da ake masa, wadanda aka gabatar tun bayan tsige shi daga Firaminista a shekarar bara. 

Kafin kama Imran Khan dai sai da aka shafe fiye da watanni ana rikici tsakanin jami’an tsaro da magoya bayansa, wadanda suka tsaya kai da fata cewar ba za su bari a tsare jagoran nasu ba, matakin da suka bayyana a matsayin bi ta da kullin siyasa. 

Sa’o’i kafin tsare shi ne dai, tsohon Fira Ministan na Pakistan ya zargi wani babban jami’in sojan kasar da yunkurin yi masa kisan gilla. 

Bayanai daga biranen Karachi da Lahore sun ce, ‘Yan Sanda sun yi amfani da barkonon tsohuwa da kuma feshin ruwa domin tarwatsa masu zanga-zangar suka rufe tituna, haka kuma lamarin ya kasance a Islamabad babban birnin Pakistan da kuma garin Peshawar, da sauran garuruwa. 

Khan dai na fuskantar tuhume-tuhume da dama, cikinsu kuwa har da na almundahanar kudade da kuma alaka da ta’addanci, wadanda wasu masu sharhi suka ce gwamnatocin Pakistan da suka shude sun yi amfani da su wajen murkushe masu adawa da su. 

Ana iya hana Imran Khan rike mukamin gwamnati idan har aka same shi da laifi, wanda hakan zai hana shi shiga zaben da aka shirya gudanarwa a karshen wannan shekara. 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here