Ganduje ya zama shugaban APC na kasa

0
178
ganduje

Tsohon gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya zama sabon shugaban jam’iyyar APC mai mulki ta kasa.

An zabe shi ne a taron kwamitin zartaswa na kasa karo na 12 da aka gudanar a Abuja.

Jaridar HAUSA24 ta ruwaito cewa nadin nasa ya biyo bayan murabus din Sanata Abdullahi Adamu ne a watan jiya.

Shugaba Bola Tinubu ya nuna sha’awar Ganduje ya gaji Adamu.

Haka kuma, Ajibola Bashiru, tsohon kakakin majalisar dattawa, an tabbatar da shi a matsayin sakataren jam’iyyar na kasa a hukumance.

Taron na NEC ya shaida halartar mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, da gwamnoni da dama, da manyan jiga-jigan jam’iyyar tare da Tinubu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here