Shugabannin tsaro 10 na ECOWAS sun gana a Abuja

0
149

Manyan hafsoshin tsaro na kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ECOWAS na taro a Abuja kan halin da ake ciki a Nijar inda sojoji suka hambarar da zababbiyar gwamnatin Mohammed Bazoum.

Taron dai na samun halartar kasashe 10 da suka hada da Najeriya da Saliyo da Togo da Laberiya da Ghana da Gambia da Cote D’voire da Cape Varde da Benin da kuma Senegal.

Wadanda ba su halarci taron sun hada da Mali da Nijar da Guinea da Guinea Bissau da kuma Burkina Faso.

A ranar Lahadin da ta gabata shugabannin kungiyar ECOWAS sun kakabawa Nijar takunkumi tare da gargadin cewa za su yi amfani da karfi wajen maido da hambararren shugaban kasar.

Kungiyar ECOWAS ta bai wa gwamnatin mulkin sojan Nijar mako guda da su fice daga fagen daga tare da baiwa shugaba Bazoum damar komawa bakin aiki.

Tun da farko dai, gwamnatin mulkin sojan ta yi gargadin cewa za ta bijirewa duk wani shiri na kai hari ga Nijar daga kungiyar ECOWAS ko kuma wata kasa ta Yamma.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here