Bagudu,Lalong,Matawalle sun shiga jerin ministocin da Tinubu ya sake nadawa

0
176
Bagudu,Lalong,Matawalle
Bagudu,Lalong,Matawalle

Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya Godswill Akpabio ya bayyana ƙarin sunayen mutum 19 da Shugaba Bola Tinubu ya aika musu domin naɗa su ministoci.

Cikin jerin har da tsofaffin gwamnoni biyar da suka haɗa da Bello Matawalle na Zamfara, da Atiku Bagudu na Kebbi, da Gboyega Oyetola na Osun.

Sauran tsofaffin gwamnonin su ne Ibrahim Geidam na Yobe, da Simon Lalong na Jihar Filato.

Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa Femi Gbajabiamila ne ya kai wa Majalisa sunayen a madadin shugaban ƙasa bayan 28 da ya bayar tun farko.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here