Shari’ar zaɓen gwamnan kano: Abba Gida-Gida ya daukaka kara akan shaidan APC

0
186

Gwamnan jihar kano Abba Kabir Yusuf ya daukaka kara akan ra,ayin kotun Sauraron Korafe korafen Zabukan Gwamna wanda ta baiwa APC dama ta kirawo wani masani Dr. Aminu Idris Harbau Shaidarta na 32, don bayar da shaida.

Abba Kabir din dai ya shigar da karar ne da dalilai shida na daukaka kara, ya na zargin cewar kotun ta yi kuskure saboda baiwa masanin Shaidar dama bayan APC bata Mika bayanan sa ba kwanaki goma bayan da aka kammala share Fagen shiga shari’a.

Abba Kabir Yusuf ya na rokon kotun daukaka karar da ta rushe duk bayanan da Dr. Harbau yayi a gaban kotun inda take cewar ba,a kirawo shi ba bisa ƙa’ida.

Majiya ta shaidawa Kadaura24 ta rawaito cewar tuni aka sabunta bangarorin Sharia da takardun daukaka kara.

Kowane lokaci, kotun zata sanar da lokacin da zata saurarin wannan kara da Abba Kabir Ya daukaka ya na zargin kotun sauraron korafe-korafe zaben gwamna Kano da tabka kuskure.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here