Sadio Mane na shirin tafiya Al Nassr ta Saudiyya

0
141

Rahotanni sun ce fitaccen dan wasan Senegal Sadio Mane yana dab da tafiya Saudiyya watanni 13 bayan ya bar Liverpool zuwa Bayern Munich.

Rahotanni da dama sun ce dan wasan ya riga ya amince da tayin da kungiyar Al Nassr ta yi masa.

Idan hakan ya tabbata, zai rika murza leda da ‘yan wasa irin su Cristiano Ronaldo, Tonaldo da Marcelo Brozovic da kuma Alex Telles.

Bayan ya koma Bayern Munich daga Liverpool a bara, abubuwa ba su yi Mane kyau ba a kakar da ta wuce.

Ya zura kwallaye bakwai a raga a wasannin Bundesliga 25 da ya yi, kuma daga bisani sabon kocin kungiyar Thomas Tuchel ya rika ajiye shi a benci.

Hakan ne ya sa Bayern take ganin zai fi mata kyau ta sayar da dan wasan saboda ta rage asara.

Idan Mane ya bar Liverpool, kungiyar za ta yi asarar Yuro miliyan 7.6 daga cikin Yuro miliyan 35.1 da ta kulla yarjejeniya da shi a kakar bara.

Tun da farko Liverpool ta karbi Yuro miliyan 27.5 daga hannun Bayern, amma yanzu da wuya ta samu ragowar Yuro miliyan 7.6.

Har yanzu dan wasan gaban zai iya bayar da gudunmawa sosai a babbar kungiya, ko da yake kwazonsa ya ragu a ‘yan shekarun nan.

Bayern Munich za ta iya samun riba daga sayar da Mane – saboda akwai rahotannin da ke cewa an taya dan wasan a kan Yuro miliyan 30.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here