Juyin mulki: Sojoji sun nada Abdourahmane Tchiani shugaban kasar Nijar

0
160

Sojojin da suka yi juyin mulki a kasar Nijar sun sanar da Janar Abdourahmane Tchiani a matsayin sabon shugaban gwamnatin rikon kwarya.

Janar Abdourahmane Tchiani mai shekaru 62 shi ne Kwamandan Rundunar Tsaron Shugaban Kasa, wadda ta kifar da gwamnatin Shugaba Mohamed Bazoum, mai shekaru 64 a ranar Laraba.

Sanarwar da rundunar sojin ta yi a ranar Juma’a ta tabbatar da kifar da gwamnatin Bazoum, tare da ayyana Janar Tchiani a matsayin “Shugaban Majalisar Tsaron Kasa”.

A shekarar 2015 ne aka fara nada Janar Abdourahmane Tchiani dan asalin yankin Tillaberi da ke Yammacin kasar, wanda kuma amini ne ga tsohon shugaban kasar Mahamadou Issoufou – wanda ya mika wa Bazoum mulki a shekarar 2021.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here