‘Yan Nijar sun yi zanga-zangar adawa kan yunkurin juyin mulki a kasar

0
149

Wasu magoya bayan Shugaba Mohamed Bazoum da wasu ‘yan kasar sun gudanar da zanga-zangar adawa da yunkurin juyin mulkin da aka so yi a Jamhuriyar Nijar a ranar Laraba.

Mutane da dama ne suka fito don yin zanga-zangar a babban birnin kasar Yamai da Tahoua da Zinder, suna masu nuna goyon bayansu ga dorewar dimokuradiyya.

Masu zanga-zangar sun je majalisar dokokin kasar domin jaddada bukatarsu ta ganin wanzuwar mulkin dimokuradiyya.

Tun da fari a ranar Laraba Fadar shugaban kasar Nijar a wasu sakonni da ta wallafa a shafin Twitter ta tabbatar da cewa wasu sojojin fadar sun tayar da yamutsi.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ambato wasu majiyoyi na soji suna cewa sojojin run rufe dukkan hanyoyin da ke shiga fadar ta shugaban kasa a ranar Larabar.

Masu gadin fadar shugaban kasar sun yi ta harbi da bindiga sama don gargadi ga masu zanga-zangar adawa da tsare Shugaba Mohamed Bazoum da suke ci gaba da yi, kamar yadda AFP ya rawaito.

Masu zanga-zangar sun yi kokarin durfafar fadar shugaban kasar inda masu gadin fadar ke tsare da Shugaba Bazoum, amma aka tarwatsa su da harbe-harben bindiga sama.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here