Mataimakin shugaban jam’iyyar APC ya yi murabus

0
154

Mataimakin shugaban jam’iyyar APC na kasa yankin (Arewa maso Yamma) Salihu Mohammed Lukman, ya yi murabus.

Lukman, a wata wasika mai dauke da kwanan wata 26 ga watan Yuli wacce ya aike wa mukaddashin shugaban jam’iyyar na kasa, Sanata Abubakar Kyari, ya ce ya yi murabus ne sabida tsarin da jam’iyyar ke shirin dauka ya saba da manufar kafa jam’iyyar.

Ya ce, zai zama kunar bakin wake ne a maye gurbin Sanata Abdullahi Adamu, tsohon shugaban jam’iyya mai mulki ta kasa da tsohon gwamna Kano, Abdullahi Ganduje.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here