Kudirin samar da kwalejin tarayya a Rano ya samu karatu na farko a majalisa

0
136

Majalisar Wakilai ta Najeriya ta gudanar da karatu na Farko ga Kudirin Samarda Kwalejin Tarayya ta Fasahar Yada Labarai da Sadarwa a Karamar Hukumar Rano dake Yankin kudancin Jihar Kano.

Kudirin Wanda Wakilin kananan hukumomin Rano, Kibiya da Bunkure a Majalisar ya gabatar na da bukatar Samarda wannan Kwaleji(Collage of Information and Communication Technology) wacce kwata kwata babu itinta a Yankin arewa maso yammacin Kasar nan.

Akawun Majalisar Wakilan ta kasa ne ya karanta kudirin a matakin farko shugaban Majalisar Kuma Rt Hon Tajudden Abbas ya buga gudumar amincewa da karatun farkon da hakan ke nuna kudirin ya shiga jerin ayyukan da Majalisar zata aiwatar a nan gaba.

Haka Kuma a wannan rana ta Laraba, Majalisar Wakilan ta gudanar da karatu na uku ga kudurori guda biyu da Dan Majalisar Rt Hon Kabiru Alhassan Rurum ya gabatar a Majalisa ta 9 data shude.

Kudurorin sun hadar da na Samarda Kwalejin tarayya ta Fasaha(Federal Polytechnic Rano) da Kuma Babban Cibiyar harkokin lafiya ta tarayya(Federal Medical Center Rano).

A ganawarsa da Manema Labarai bayan kammala zaman na yau,,Rt Hon Kabiru Alhassan Rurum yace kudirorin guda biyu na jiran ayi musu zaman karshe ne a majalisar tasu sannan a mikawa Majalisar Dattawan Dan Neman sahalewar ta kafin akai ga aiwatar da wadannan makarantun da Cibiyar Kula da Lafiya.

Rurum din yace bazai gajiya ba wajen farautowa Al’ummarsa Ayyukan More rayuwa a wakilcin nasa har sai ya ga Yankin da mutanen sa sun samu bunkasa yadda ya kamata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here