Yadda matasa suke shaye-shaye a Kano na damun mu matuka – Sarkin Kano

0
147

Mai martaba sarkin kano Alhaji Aminu Ado Bayero, yace masarautar Kano ta damu da yawan samun karuwar matasa da yan mata wajen shan miyagun kwayoyi da ake samu a jihar Kano.

Alhaji Aminu Ado ya tabbatar da cewar masarautar kano a shirye take domin aiki da jami’an tsaro, da kungiyoyin al’umma domin kawo karshen matsalar shan miyagun kwayoyi.

Sarkin ya bayyana haka ne lokacin da gamayyar kungiyoyin arewacin kasar nan karkashin jagorancin Sharif Nastura suka kai masa ziyara a fadar sa.

A nasa jawabin shugaban kungiyar Initiative For Community Action Againts Drugs Abuse, Sharif Nastura yace sunzo fadar ne domin sanar da sarkin kan shirin taron fadarkar da al’umma kan illar shaye shayen miyagun kwayoyin da matasa suke yi.

Ya kuma shawarci matasa wajen kaucewa ta’ammali da kwayoyin duba da yadda hakan na iyan illa ga rayukan al’umma.

A wani ci gaban labarin kuma shugaban cibiyar yan jaridu ta kasa karkashin jagorancin Alh Mukhtar Zubair Sa’ad ta bawa mai martaba sarkin kano Alhaji Aminu Ado Bayero takardar karramawa domin zama cikakken mamba, a kungiyar bisa kokarin da yake wajen ci gaban al’ummar kasar nan.

Shugaban cibiyar yan jaridu Alhaji Muktar Zubair Sa’ad ya kuma tabbatar da cewar cibiyar ta sami nasarori a fannika daban daban musamman a fannin wayar da kan al’ummar kasar nan.

A nasa jawabin mai martaba sarki kano Alhaji Aminu Ado Bayero yace masarautar zata ci gaba da basu hadin kai bisa irin kokarin da suke wajen taimakawa al’umma.

Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya nada sabon dagacin shekar barde Alhaji Abubakar Musa Zakari.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here