CBN ta kara wa masu cin bashin banki kudin ruwa

0
166

Babban Bankin Najeriya, CBN, ya ƙara yawan kuɗin ruwa da kashi 0.2 cikin 100 da masu cin bashi daga bankuna za su dinga biya a ƙasar.

Hakan na nufin yanzu duk wanda ya ci bashin banki zai biya kashi 18.75 na kuɗin da ya karɓa, maimakon 18.5 da aka saka a watan Mayu da ya gabata.

CBN ya ɗauki matakin ne da zimmar daƙile hauhawar farashi ta hanyar rage wa mutane sha’awar mallakar zunzurutun kuɗi. 

Muƙaddashin Gwamnan CBN Fola Shonubi ya ce bankin ya cimma wannan matsaya ce bayan la’akari da tasirin cire tallafin mai, da na haɗe kan kasuwar canjin kuɗi, da kuma yunƙurin gwamnati na rarraba kayan tallafi. 

Wannan ne ƙari na farko da Shugaba Bola Tinubu ya yi bayan sauran matakan tattalin arziki da ya ɗauka tun bayan hawansa mulki a watan Mayu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here