Davido ya goge faifan bidiyon da ya janyo ce-ce-ku-ce

0
141

Fitaccen mawaki a Nijeriya, David Adeleke, wanda aka fi sani da Davido, ya goge faifan bidiyon wata waka da ta janyo ce-ce-ku-ce a shafukan sada zumunta da yaron aikinsa Logos Olori ya yi bayan ya fuskanci tsangwama a shafukan sada zumuntar.

A ranar Asabar, Davido ya fuskanci suka da tsangwama daga al’ummar Musulmai da yawa a shafukan sada zumunta sabida hada hotunan wakar faifan bidiyon da wurin bauta, wacce yake shirin fitar wa nan gaba kadan.

A Bidiyon wakar, ya nuna wasu gungun mazaje masu Sallah, dukkansu sanye da fararen jallabiya, suna cikin Sallah sai mai waka ya fara, ba zato ba tsammani wurin Ibada ya koma filin rawa da waka.

Al’ummar Musulmai sun zargi mawakin da rashin mutunta addininsu ta hanyar hada ayyukansu na addini da waka da raye-raye.

Sun kuma yi kira gare shi da ya goge faifan bidiyon tare da neman gafara.

Fitattun ‘yan Nijeriya irin su Bashir Ahmad da Ali Nuhu duk sun kalubalanci mawakin kan rashin mutunta addinin Musulunci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here