Ahmed Musa ya rage farashin litar man fetur zuwa N580 a gidan man shi 

0
166

Kyaftin din Super Eagles Ahmed Musa ya sanar da rage farashin litar man fetur a gidan man shi dake jihar Kano.

Ahmed Musa yayi ragin ne sakamakon tsadar da man fetur din yayi a kwanakin nan, biyo bayan karin farashi da aka samu daga N540 zuwa 620 kan kowace liter.

Ya sanar da wannan labarin ne a shafin sa na tuwita a yau kuma yace radin kansa ne kawai yasa yayi hakan domin saukakawa mutane halin da suke ciki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here