Matakai 6 da Gwamnatin Tarayya za ta dauka don samar da saukin rayuwa

0
139

Majalisar kula da Tattalin Arziƙi a Najeriya ta sanar da wasu sabbin matakai da gwamnati za ta ɗauka don samar wa ‘yan ƙasar sauƙin rayuwa sanadin wahalhalun janye tallafin man fetur.

Majalisar ta sanar da matakan ne a ƙarshen taron wata-wata da ta yi a ƙarƙashin jagorancin mataimakin shugaban ƙasar Kashim Shettima.

Taron na tsawon kimanin sa’a shida ya fi mayar da hankali a kan batutuwa guda biyu da suka fi tasiri wajen jefa ‘yan ƙasar cikin mawuyacin hali. Wato janye tallafin mai da kuma karyewar darajar Naira.

Bayan tafka muhawara da musayar yawu, taron ya amince da ɗaukar wasu matakai na gaggawa domin tsamo ‘yan Najeriya musamman mafi ya rauni daga cikin halin da suka shiga. Daga ciki akwai buƙatar kowacce jihar ta tsara yadda za ta samar wa jama’arta sauƙi ko dai ta hanyar raba tallafin kuɗi ko kuma ta hanyar da ta fi dacewa.

Haka ma an amince da bai wa ma’aikatan gwamnati tallafin kuɗi a kan albashinsu, tsawo wata shida, sannan kowacce jiha ta tabbatar ta biya ma’aikata da ‘yan fansho dukkan basukan da suke bi.

Waɗannan in ji majalisar za a aiwatar da su ne ta hanyar amfani da rarar kuɗin da gwamnati za ta samu saboda janye tallafin man fetur da kuma daidaita harkar canjin kuɗi.

Bugu da ƙari, taron ya amince da aiwatar da wani tsari na sauya makamashin da ababen hawa suka fi amfani da su daga man fetur wanda ya yi tsada yanzu zuwa wani nau’in iskar gas da ake kira CNG a taƙaice wanda Najeriya ke da shi mai tarin yawa kuma ga arha.

Jihohin ƙasar sun amince za su fara juya motocin jigilar ma’aikata zuwa masu amfani da iskar gas.

Amma duk waɗannan matakai, sai bayan an aiwatar da shirin raba kayan abinci ga ɗaukacin jihohin ƙasar domin sauko da farashinsa, a cewar Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi.

Majalisar dai ta ce tana sane da mawuyacin halin da ‘yan ƙasar ke ciki don haka ɗaukar waɗannan matakai sun zama wajibi domin kaucewa yanayin da wahala za ta tura ‘yan ƙasar bango har su yi bore.

Wani babban batu da ‘yan kasar ga alama suke son su ji matsayar majalisar a kai shi ne amincewa ko akasin haka da bukatar ƙarin albashi ga ma’aikata zuwa aƙalla N200,000 kamar yadda ‘yan kwadago ke nema, sai dai ga alama babu wata matsaya da aka cimma a kan haka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here