Gwamnatin Kano ta dauki hayar Femi Falana kan shari’ar bidiyon Dala

0
153

Hukumar Karba Korafe-Korafe da Yaki da Rashawa ta Jihar Kano (PCACC), ta sanar da daukar hayar babban lauyan nan mai fafutikar kare hakkin dan Adam, Femi Falana.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, Hukumar PCACC ta dauki babban lauyan ne domin wakiltar ta a takaddamar bidiyon dala da ake tuhumar tsohon Gwamnan Jihar, Abdullahi Umar Ganduje da zargin karbar na goro.

Lauyan PCACC, Usman Fari ne ya bayyana hakan bayan soma sauraron shari’ar wanda kuma kotu ta dage zuwa ranar 25 ga watan Yuli.

Dage zaman na zuwa ne bayan da lauyan Ganduje, Basil Hemba ya shaida wa kotun cewa yana bukatar karin lokaci domin tattaro hujjojin da zai gabatar na kare tuhumar da ake yi wa wanda yake wakilta.

Aminiya ta ruwaito cewa, an yi tsammanin saukar Babban Lauya Femi Falana a Kano da safiyar wannan Juma’ar, sai dai shi da tawagarsa sun gamu da cikas sakamakon rashin tashin jirginsu.

Ana iya tuna cewa, a makonnin bayan nan ne dai wata Babbar Kotun Tarayya ta amsa rokon Ganduje na hana gayyatarsa ko kama shi domin bincikarsa kan zargin karbar na goro a wani hoton bidiyo da aka nada wanda aka fi sani da ‘bidiyon dala.’

A shekarar 2017 ne, jaridar Daily Nigerian da ake wallafawa a intanet, ta fitar da jerin bidiyon da ke nuna wani mutum wanda ta yi zargin cewa Ganduje ne yake karbar damin daloli daga hannun wasu ’yan kwangila yana zubawa a aljihu.

Haka kuma, Ganduje ya shigar da kara a gaban Mai Shari’a S.A Amobeda na Babbar Kotun Tarayya yana neman a dakatar da Hukumar Yaki da Rashawar daga bincikarsa kan kudaden Kananan Hukumomi na Naira biliyan 100 da aka nema aka rasa a zamanin mulkinsa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here