Gwamnati tarayya ta ninka kudin daliban makarantun sakandire

0
168

Gwamnatin Tarayya ta sanar da karin fiye da kashi 100 na kudin makarantar sabbin daliban sakandire da ke karkashinta da aka fi sani da Unity Colleges ko kuma Federal Government College (FGC).

Da wannan lamari, a yanzu sabbin dalibai za su rika biyan N100,000 sabanin N45,000 da sabbin dalibai na bara suka biya.

Hakan dai na kunshe cikin wata takarda mai lamba ADF/120/DSSE/I da aka fitar daga Ofishin Daraktar Kula da Makarantun Sakandire a Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya, Hajiya Binta Abdulkadir.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, karin kudin zai shafi duk ababe da harkokin karatun daliban ciki har da kudin kwana, littafai na rubutu da karatu, kayan makaranta, wasanni da sauransu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here