An harbe mutum 2 yayin da suke wawason kayan masarufi a Taraba

0
152

Wasu mutane biyu sun rasa rayukansu a lokacin da wasu gungun matasa suka fasa wani rumbun amfanin gona a Jalingo, babban birnin Jihar Taraba.

Lamarin ya auku ne da tsakar daren Juma’a inda wasu matasa masu yawan gaske suka fasa wani babban rumbun kayan amfanin gona mallakan wani dan siyasa mai suna Dokta Jugulde suka yi awon gaba da buhunan shinkafa da Masara da wasu kayayyaki.

Wani mai gadin rumbun wanda ya nemi a sakaya sunansa ya ce da misalin karfe 10:40 na daren jiya suka ga wasu matasa masu yawa na kokarin fasa rumbun.

Ya ce ganin haka sai aka gaggauta shaida wa jami’an ’yan sanda da soji, amma kafin isowar jami’an tsaro matasan sun riga sun fasa rumbun sun soma wawason kayayyaki wadanda suka hada da masara da shinkafa da takin zamani da maganin feshi.

Ya ce jami’an tsaro sun yi kokarin hana matasan dibar kaya a rumbun amma haka bai yiwu ba, lamarin da ya sa suka soma harbe-harbe har ta kai ga mutuwar mutum biyu nan take.

Binciken wakilin Aminiya ya nuna cewa an sace daruruwan buhunan shinkafa da Masara da wasu sauran kayayyaki na dubban nairori.

Kazalika, an ruwaito cewa matasan sun fasa wasu karin rumbunan wadanda ke kusa da wurin na farko, inda nan ma suka sace wasu kayayyakin na dubban nairori.

Bayanai sun ce an taba fasa rumbun dan siyasar lokacin zanga-zangar EndSARS, inda aka sace kayayyaki na miliyoyin Naira.

Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Taraba, SP Usman Abdullahi ya bayyana wa Aminiya cewa bai sami cikakken bayani kan wannan lamari ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here