Rundunar sojin sama ta kashe yan fashin daji 22 a Katsina

0
144
Sojin sama

Rundunar sojin  sama ta ƙasa ta  kashe ƴan fashin daji 22 yaran marigayi Abdulkareem Boss a jihar Katsina.

Dakaraun Operation Hadarin Daji ne suka kai hare-haren a Batsari da Sola Poli II dake ƙananan hukumomin Batsari da Jibia.

Majiyar Aminiya ta ce ƴan fashin da aka harbe su ne ke kai hare-hare tare da garkuwa da mutane a ƙaramar hukumar Ƙanƙara.

A ranar Agusta 6, 2022 ne rundunar sojin sama ta ƙasa ta hallaka Abdulkareem Boss da wasu daga cikin yaransa a Dajin Rugu dake jihar Katsina.

Marigayi Abdulkareem Boss ne ake zargi da kisan kwamanda shiyyar Dutsin-ma na rundunar ƴan sanda a ranar Yuli 5, 2022.

Kakakin rundunar sojin sama, Air Commodore Edward Gabkwet ya tabbatar da kashe ƴan fashin dajin sai dai bai bada bayanin farmakin ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here