Kaduna: Hukumar lafiya ta tabbatar da bullar cutar Diphtheria a Kafanchan

0
148

Ma’aikatar lafiya ta jihar Kaduna ta tabbatar da bullar Diphtheria a garin Kafanchan da ke karamar hukumar Jema’a ta jihar.

Tabbatar da bullar cutar ya biyo bayan samun wasu rahotanni daga mazauna yankin Takau a Kafanchan A da Kafanchan B da ke nuna wasu alamomi kamar sarkewar numfashi da zazzabi mai zafi da tari d kasala da ciwon makogwaro da kuma kumburin wuya

Idan dai za a iya tunawa, LEADERSHIP a ranar Alhamis ta bayar da wani rahoto kan bullar wata bakuwar cuta a yankin Kafanchan, inda ta kashe yara akalla 10 masu shekaru tsakanin uku zuwa 10.

Sakataren yada labaran gwamnan Jihar, Muhammad Lawal, a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a, ya bayyana irin asarar rayuka da aka yi a yankunan da lamarin ya shafa, ya kuma ce nan take gwamnan jihar ya umarci ma’aikatar lafiya ta jihar da ta tura tawagar kai agajin gaggawa don gudanar da bincike kan lamarin.

Sanarwar ta ce wani rahoto na farko da ma’aikatar ta fitar ya nuna cewa an samu bullar cutar Diphtheria a Kafanchan a farkon watan Yuli, 2023.

Gwamna Sani, ya yabawa jami’an kiwon lafiya kan gaggawar daukar matakin dakile cutar tare da kokarin kawar da ita.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here