Man United ta maye gurbin De Gea da Andre Onana

0
140

Manchester United ta kammala sayen gola ɗan asalin Kamaru, Andre Onana a kan £47.2m (€55m) daga Inter Milan.

Ɗan wasan na Kamaru, mai shekara 27, ya rattaba hannu kan kwantiragin shekara biyar, tare da zaɓin tsawaita wa’adin zamansa tsawon wata 12.

Yarjejeniyar ta kai darajar £43.8m kai-tsaye da kuma fam miliyan 3.4 a cikin tsarabe-tsarabe, kuma tsohon mai tsaron ragar na Ajax yana shirin shiga cikin tawagar United a ziyarar da za ta kai Amurka.

Onana zai maye gurbin David de Gea a matsayin mai tsaron ragar United na farko, sanadin tafiyar ɗan ƙasar Sifaniyan a watan Yuli, lokacin da kwantiraginsa ya ƙare bayan shekara 12.

Onana ya taka leda a ƙarƙashin kocin United Erik ten Hag na tsawon shekara bakwai da rabi a Ajax, inda ya lashe kofunan lig guda uku, kuma an taɓa dakatar da shi tsawon wata tara a 2021 bisa laifin shan ƙwaya.

Bayan ya koma Inter kyauta a watan Yulin 2022, Onana ya taimaka wa ƙungiyar ta Italiya kai wa ga wasan ƙarshe na gasar zakarun Turai, inda suka sha kashi da ci 1-0 a hannun zakarun Premier Manchester City.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here