Hukumar kwallon kafar Kamaru ta dakatar da wasu ‘yan wasan kasar

0
155

Hukumar da ke sanya ido a harkokin kwallon kafar Kamaru ta dakatar da ‘yan wasan wasu tawagogin kwallon kafar kasar takwas saboda shirga karya a shekarunsu.

Hukumar ta bayyana haka ne a sakon da ta wallafa ranar Laraba a shafinta na Twitter.

Sai dai sanarwar ba ta fadi tsawon lokacin hukuncin da aka yi musu ba.

Ta ce ‘yan kwallon sun fito ne daga tawagogi daban-daban da ke murza leda a cikin gida.

“Hudu daga cikinsu sun fito ne daga tawagar Nyom II academy, 1 daga tawagar Volcan of Noun yayin da uku suka fito daga taewagar Union sportive of Abong-Mbang da ke Lardin Gabas”, in ji sanarwar.

‘Yan wasan da aka dakatar su ne Alex Ngani Ngani, Fabrice Faha, Michel Mohamed Bengono Bekono, Santo Kisito Elouna Elouna, Eric Toko Toko, Beaudelaire Bodamba, Wadjiri Haman da Wilfred Yaan Yann Yatti Yatti

Daga yanzu ba za su kara fafatawa a wata gasa ba sai wa’adin da aka dibar mus ya cika, a cewar sanarwar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here