Ganduje ya tura sunan Gawuna a masa mukamin minista

0
172

A yayin da ake dakon sunayen ministoci, wasu rahotanni sun ce tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya mika sunan tsohon mataimakinsa kuma dan takarar jam’iyyar APC a zaben 2023, Nasiru Yusuf Gawuna domin a masa mukamin minista.

Wata majiya ta bayyana wa NIGERIA TRACKER cewar Ganduje ya aike da sunan tsohon mataimakin nasa.

A baya dai wasu jaridu sun ruwaito cewa an soke sunan Ganduje daga cikin wadanda ake dakon yi wa mukamin minista.

Sai dai an bayyana cewa shugaban kasa Bola Tinubu ya bukace shi da ya zabo wadanda suka dace daga Kano.

Wannan al’amari ya kawo karshen jita-jitar rashin sanya sunan Nasiru Yusuf Gawuna a cikin jerin sunayen ministocim da ake dakon fitowar sunayensu.

Majiyar ta kuma shaida wa jaridar cewa ana tunanin Ganduje zai maye gurbin Abdullahi Adamu a matsayin shugaban jam’iyyar APC na kasa na rikon kwarya.

Ya kuma mika sunan Rabi’u Suleiman Bichi da tsohon sakataren gwamnatin jihar Kano, Alhaji Usman Alhaji domin yi musu mukami a gwamnatin tarayya.

Sai dai ana ci gaba da tafka muhawara a siyasar Kano, tsakanin tsagin Kwankwasiyya da kuma tsagin tsohon Gwamna Ganduje, inda dukkaninsu ke neman ganin nasu ya samu mukami a gwamnatin shugaba Tinubu.

Yanzu haka tsagin Kwankwasiyya ne ke rike da gwamnatin jihar Kano a karkashin jam’iyyar NNPP.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here