Farashin danyen mai ne ya haifar da karin farashin man fetur – NNPC

0
161
man fetur
man fetur

Shugaban Kamfanin Man Fetur na Kasa (NNPCL), Mele Kyari, ya danganta tashin farashin man fetur daga Naira 540 zuwa Naira 617 da yanayin kasuwa.

Ya bayyana haka ne ga manema labarai a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja a ranar Talata, bayan wata ganawa da Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima.

Kyari, ya ce karin kudin da aka samu ba shi da alaka da karancin man fetur.

“Farashin ya danganta da yanayin kasuwa. Wannan shi ne ma’anar tabbatar da cewa kasuwa ta daidaita kanta. Farashin zai iya hawa kuma a wani lokacin zai iya sauka. Ba batun samar da mai ba ne.

“Idan ka je kasuwa, ka sayi kaya, za ka zo kasuwa ka sayar da shi a kan farashin da kasuwa ta ke. Ba shi da alaka da wadatarsa. Mun samu sama da kwanaki 32 muna shigo da mai. Wannan ba matsala ba ce,” in ji shi.

Kyari, ya ce abu ne mai kyau ga ‘yan kasuwa su daidaita farashin.

“Ina tabbatar wa ’yan Najeriya cewa wannan ita ce hanyar da ta dace don daidaita farashin yanayin kasuwa. Ba ni da cikakken bayanai a wannan lokacin, amma na san cewa wannan ba mai dorewa ba ne. Na san cewa kamfanoni da yawa sun shigo da man fetur kuma komai zai daidaita nan bada jimawa.”

Martanin nasa na zuwa ne baya da wasu gidajen man NNPC aka wayi gari sun kara farashin man fetur daga 540 zuwa 617 a Abuja.

A nasa bangaren, babban jami’in hukumar kula da harkokin man fetur ta kasa, Farouk Ahmed, ya ce karin farashin ya faru ne sakamakon tashin farashin danyen mai.

Ya kuma ba da misali da sauye-sauyen farashin kaya tare da wasu karin kudadeen da masu shigo da kaya ke yi.

“Don haka, idan kuka ce yanayin kasuwa ya yi aiki, wannan shi ne ainahin abin da ake nufi, ya hau ko ya sauka… Kuna ganin farashin danyen mai ya tashi.

“Cikin mako daya farashin danyen mai ya kai kusan Dala 70 kan kowace ganga. Yanzu, yana kan Dala $80 kowace ganga.

“Don haka, babu shakka farashin danyen mai ne ya haifar da karin farashin kayayyaki. Kamar yadda masu shigo da kayayyaki ke shigo da su, suna dogara ne akan farashin shigo da kayayyaki da sauran abubuwan kashe kudi ta fuskar rarraba su a cikin gida,” cewar Ahmed.

A ranar Talata ne ‘yan kasuwa mai masu zaman kansu suka tabbatar da karin farashin man fetur, yayin da suka bayyana cewa duk wani canjin farashin da gidajen man NNPC suka yi na nuni da tashin farashin man.

A jawabinsa na farko a ranar 29 ga watan Mayu, shugaba Bola Tinubu ya sanar da dakatar da tallafin man fetur.

Wannan ya haifar da hauhawar farashin man fetur daga Naira 198 kan kowace lita zuwa sama da Naira 500 kan kowace lita a ranar 30 ga Mayu, 2023.

AMINIYA

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here