Tinubu zai magance matsalar tsaron arewa maso yammacin Nijeriya — Shettima

0
165

Mataimakin shugaban Nijeriya Kashim Shettima ya ce amfani da karfin soji kadai ba zai magance matsalar ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa a Arewa maso Yammacin kasar ba.

TRT ta ce, Shettima ya bayyana haka ne ranar Lahadi yayin wata ziyarar ta’aziyya da ya kai jihar Kano da ke arewacin kasar.

Yankin na Arewa maso Yammacin Nijeriya ya dade yana fama da matsalar hare-haren ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane, wadanda kan bi mutane har gida ko su tare kan hanya, ko kuma su je makarantu su sace dalibai.

Gwamnatin kasar ta dauki matakai daban-daban domin magance matsalar, ciki har da yin ruwan bama-bamai da jiragen sojin sama kan maboyar ‘yan bindigar.

Sai dai duk da wadannan matakai, matsalar na ci gaba da ta’azzara musamman a jihohin Zamfara da Kaduna, inda ‘yan bindiga suka hana mutane sukuni.

Pulaku

Kashim Shettima ya ce nan ba da jimawa ba gwamnatin Bola Ahmed Tinubu za ta bullo da wani shiri da ta yi wa lakabi ‘pulaku’ don shawo kan hare-haren da ake alakantaka da makiyaya a yankin.

“Idan dai ba so muke mu ci gaba da zubar da jini ba, ta ya kamata mu sani cewa amfani da karfin soji ba zai kawo karshen rikicin Arewa maso Yammaci ba.

Dole a bugi jaki sannan a bugi taiki. Nan da makonni masu zuwa, Shugaba Bola Tinubu zai kaddamar da tsarin magance wannan matsala mai suna Pulaku wanda zai magance matsalolin da ‘yan uwanmu Fulani suke fuskanta a Arewa maso Yamma; zai nemo silar rikicin ‘yan bindiga da hare-hare a kasar nan” da zummar magance shi, in ji shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here