Kyari ya maye gurbin Adamu ‘matsayin shugaban jam’iyyar APC na kasa’

0
127

Mataimakin shugaban jam’iyyar APC na kasa shiyyar Arewa, Sanata Abubakar Kyari, ya zama shugaban rikon jam’iyyar APC na kasa.

Hakan ya biyo bayan murabus din da Sanata Abdullahi Adamu ya yi a matsayin shugaban jam’iyyar na kasa.

Kamar yadda kundin tsarin mulkin jam’iyyar ya tanada, idan shugaban jam’iyyar na kasa ya yi murabus, mataimakin shugaban jam’iyyar na kasa daga shiyya ne zai karbi ragamar mulki.

Kyari ya jagoranci wasu mambobin kwamitin gudanarwa na kasa (NWC) zuwa wani taro da ke gudanarwa a halin yanzu a sakatariyar jam’iyyar ta kasa da ke Abuja cikin tsauraran matakan tsaro.

Wadanda suka shiga taron da Kyari sun hada da Mataimakin Shugaban Kasa Jam’iyyar daga yankin Kudu, Emma Enukwu da takwaransa na yankin Arewa Maso Yamma, Salihu Lukman da Kuma Mataimakin Shugaban Kasa na shiyyar Arewa Maso Gabas, Salihu Mustapha da takwaransa na Arewa Ta Tsakiya, Muazu BawaBawa da Mataimakin shugaban na Kudu maso Yamma, Issacs Kekemeke da Mataimakin shugaban na kudu maso gabas , Ejoroma Arodiogu da mataimakin sakataren Jam’iyyar na kasa, Barr. Festus Fuanter.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here