Cutar Dabbobi: An samu bullar Anthrax a Najeriya

0
173

Ma’aikatar Noma ta Najeriya ta tabbatar da bullar cutar Anthrax da ake samu a jikin dabbobi a karon farko a kasar.

A wata sanarwa, Babban Likitan Dabbobi na Tarayya Dr Columba Vakuru ya ce an samu bullar cutar ne a wani gidan gona a Suleja da ke Jihar Neja.

Ya ce an fara gano cutar ne a ranar 14 ga watan Yuli a jikin wasu dabbobi da suka nuna alamunta.

Likitocin dabbobi sun ce an gudanar da gwaji wanda ya tabbatar da cewa cutar ce, kuma tuni aka killace gonar.

A yanzu haka gwamnatin Jihar Neja da ta tarayyar Najeriya sun dauki matakan tabbatar da cewa an shawo kan cutar kafin ta yadu da gaggawa a kasar, in ji Gidan Talabijin na Kasa, NTA.

Gwamnatin ta kuma sanar da cewa akwai shirye-shirye da ake gudanarwa a fadin kasar na yi wa dabbobi kamar shanu da tumaki da awaki allurar rigakafin kamuwa da cutar anthrax.

Sannan za a saka ido sosai wajen ganin cutar ba ta yadu ba a gidajen gona da kasuwanni da mahauta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here