Tsadar Abinci: Yan Najeriya na cigaba da tsunduma cikin tasku

0
134

A cikin ‘yan makwannin da suka gabata, ‘yan Nijeriya sun damu a cikin halin da suka tsinci kansu na ci gaba da fuskantar hauhawan farashin kayan abinci.

Hukumar kdiddiga ta kasa ta NBS ta bayyana cewa, hauhawan farashin kayan abinci daga shekara zuwa shekara, haka farashin man girki Burondi, hatsi, Tumatir, Doya, Kifi, Nama kayan lambu da sauransu, duk sun yi tashin gwaron Zabi.

  • Acewar hukumar ta NBS,  hauhawan farashin na kayan abinci, ya karu da kashi  22.22 a cikin dari a cikin watan Afirilun 2023.
  • A bisa jin farashin kayan abinci da aka yi a wasu kasuwannin kasar nan,  a watan Yulin 2023, farashin ya nuna cewa, farashin Kwandon Tumatir daya, ya kai daga Naira   90,000 zuwa Naira 100,000, sabanin yadda a baya, ake sayar da Kwandon sa daya akan Naira 20,000.
  • Har ila yau, farashin Kwandon Tattasai wanda a baya ake sayar wa daga akan Naira 12,000 zuwa Naira 15,000,a yanzu ana sayar da Kwandon sa daya daga Naira   40,000 zuwa Naira 45,000.

Sauran kayan abincin kamar su, Taliyar Golden Penny Pasta ta Leda mai dauke da guda 20 duk katan daya ana sayar da shi kan Naira 10,200, haka Taliyar  Chicken Flabour Instant Noodles mai dauke da guda 40 a cikin Leda, ana sayar da duk katan daya kan Naira 8,000 samarin Knorr Chicken Maggi duk katan daya ana sayar da shi kan Naira 21,000.

Baya ga hauhawan farashin kayan abincin da ake ci gaba da fuskanta, an kuma danganta tashin gwaron Zabin kayan abincin akan tsadar farashin man fetur da rabar da shi da faduwar darajar Naira da kuma karancin kayan aikin gona.

Wadannan matsalolin da aka zayyano, kari da kalubalen rashin tsaro a kasar nan sun kara jefa, musamman talakawan kasar nan a cikin halin kuncin rayuwa.

A daya bangaren, wasu daga cikin manoman kasar nan, na ci gaba da fuskantar tsadar farashin kayan aikin noma, mussaman saboda tsadar farashin takin zamani da magungunan kashe kwari da rashin samun ingantaccen Irin noma da kuma rashin samar masu da kyayawan tsari, don yin noman rani.

Wani magidanci dan shekara 47 mai suna Emmanuel Ikechukwu da ke da zama a anguwar Orozo da ke Abuja wanda kuma yake da iyalai 6 ya bayyana cewa, wannan ne karo na farko a rayuwarsa da ya taba fuskantar matsin ruyuwa da ta hade masa da hauhawan farashin kayan abinci da tsadar sufuri.

A cewar Ikechukwu,“ Komai ya yi tsada a kasuwa har naji ba zan iya jurewa wa da hakan ba, ba a yi wani karin albashi ba amma farashin komai ya tashi. “

“Wannan ne karo na farko a rayuwarsa da ya taba fuskantar matsin ruyuwa da ta hade masa da hauhawan farashin kayan abinci da tsadar sufuri. “

Ya ce, me ya sa gwamnati ke kirkiro da tsare-tsaren da suke jefa rayuwar talakawan kasar nan a cikin halin kuncin rayuwar kuma shin, muna da sauran wata fata a Nijeriya kuwa  ?.

Wasu magidantan na ta hakilon samar wa iyalansu abinda za su ci, amma farashin kayan abincin, sai kara hauhawa yake yi.

Wasu gidajen da dama, sun rage yawan kayan abincin da  suke sayawa  ahalinsu, haka sun dakatar da sayen manya kayan more rayuwa da suka saba sayawa ahalansu.

Wani malamin makaranta mai suna Mallam Abubakar Usman wanda ke da zama a yankin Karu  a Abuja, shi ma kokawa ya yi akan hauhawan farashin kayan abincin.

Abubakar ya ce, a yanzu haka ni da dan uwa na, muna tsallake cin abinci har da ‘ya’yana uku saboda tashin gwaron Zabin na kayan masarufin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here