Tinubu ya gargadi masu son sake yi wa Afirka ‘mulkin mallaka’

0
144

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gargadi manyan kasashen duniya game da ci gaba da sace albarkatun nahiyar Afirka.

Ya yi gargadin ne a jawabin da ya gabatar a wurin taron shugabannin Afirka da aka yi a Nairobi babban birnin Kenya ranar Lahadi.

“Wannan duniyar da muke ciki ba ta da adalci kuma tana da rashin tabbas. Abubuwan da suka faru a tarihi da kuma abubuwan wahala da ke faruwa yanzu a duniya na zama kalubale wajen samun nasararmu,’’ in ji shugaban na Nijeriya.

Ya yi wannan jawabi ne a yayin da manyan kasashen duniya ke ci gaba da gogayya da juna domin yin tasiri a Afirka abin da masana ke gani wani bangare ne na tatsar albarkatun kasar nahiyar.

Shugaba Tinubu ya yi tir da wannan “sabon tsari na neman gindin zama a Afirka,” inda ya yi kira ga kasashen nahiyar su hada kai domin cimma manufa iri daya.

Sanarwar da kakakin shugaban kasar, Dele Alake ya fitar ta ambato shugaban Nijeriya na cewa “Ba za a maimaita abin da ya faru a baya na barnatar da albarkatun nahiyar ba.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here