Tinubu ya sanya dokar ta baci kan samar da abinci a Najeriya

0
150

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci kan batun samar da abinci a ƙasar.

Mai magana da yawun shugaban ƙasar Dele Alake, ne ya bayyana haka ga manema labarai a fadar gwamnatin ƙasar da ke Abuja.

Shugaban ƙasar ya bayar da umarnin mayar da duka al’amuran da suka shafi samar da abinci da ruwan sha, a matsayin manyan abubuwan dogaron rayuwa zuwa ƙarƙashin kulawar majalisar tsaro ta ƙasa.

Alake ya ce umarnin na cikin tsare-tsaren gwamnatin Tinubu na tabbatar da tallafa wa masu ƙaramin ƙarfi a ƙasar.

Ya ce Shugaban ya damu kan yadda farashin kayan abinci ke ƙaruwa da yadda hakan ke shafar talakawan ƙasar.

Shugaban ya kuma bayar da umarnin gaggauta bai wa manoman ƙasar taki da irin shuka domin rage musu raɗadin cire tallafin man fetur.

Ya ƙara da cewa “Dole hukumomin ayyukan gona da ta ruwan sha su yi aiki tare domin tabbatar da ingantuwar noman rani a ƙasar don tabbatar da samar wadataccen abinci a ƙasar a kowanne yanayin shekara”.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here