Ambaliyar ruwa: Gwamnan Neja ya umarci mazauna a hanyar ruwa su tashi

0
145

Gwamnatin Neja ta bukaci mazauna yankunan da suka gina gidaje a kan magudanan ruwa da su yi gaggawar tashi don kaucewa ambaliyar ruwa.

Mataimakin gwamnan jihar, Yakubu Garba ne, ya ba da umarnin a ranar Laraba, yayin ziyarar duba wasu yankuna da ambaliyar ruwa ta shafa, biyo bayan mamakon ruwan sama da aka yi a daren ranar Talata a Minna, babban birnin jihar.

Ya kuma umarci hukumar raya birane ta jihar da hukumar bada agajin gaggawa ta jihar (NSEMA) da hukumar kare muhalli ta jihar (NISEPA), da su wayar da kan jama’ar da ke zaune a magudanan ruwa domin su tashi.

“Ina jajanta wa wadanda da ambaliyar ruwan daren jiya ta shafa.

“Ya zama wajibi mu tabbatar da cewa an ceto rayuka da dukiyoyi.

“Saboda haka, na ba hukumomin gwamnati da suka dace da su duba gidaje da gine-ginen da aka yi a kan hanyoyin ruwa sannan su tashi mazauna yankunan.

“Wannan wani mataki me kaucewa sake aukuwar ambaliyar ruwaa nan gaba,” a cewarsa.

Mataimakin gwamnan ya kuma shawarci jama’a da su guji sayen filaye a magudanan ruwa don kaucewa tafka asara.

Ya kuma gardadi jama’ar jihar da su daina zubar da shara a magudanan ruwa don hakan na haifar da ambaliyar ruwa.

Shugaban Hukumar Raya Birane, Alhaji Ahmad Bako, ya ce tuni aka sanya wa gine-ginen da ke kan magudanan ruwa jan fenti da nufin rushe su.

Bako ya kara da cewa tuni aka bai wa masu wurin wa’adin tashi tare da takardar izinin rushe gine-ginen.

Wasu daga cikin wuraren da za a tayar sun hada da titin Brighter Road, Sabuwar Kasuwa da ke yankin Maitumbi, Gurara da kuma Gbaganu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here