Gwamnan Kebbi ya sallami mai bashi shawara akan wani rubutu da ya wallafa a kafar sada zumunta

0
138

Gwamnan jihar Kebbi, Nasiru Idris, ya sauke mai ba shi shawara na musamman kan harkokin matasa, Alhaji Babangida Sarki, daga nadin da ya yi masa a kan wani rubutu da ya wallafa a shafukan sada zumunta.

A cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun babban sakataren yada labaran gwamnan, Ahmed Idris, a ranar Litinin, ta bayyana cewa “Gwamnan wanda ya fusata da al’amarin ya ce mai taimaka masa ya kamata ya kasance mai kyakykyawar dabi’a da zamantakewar al’ummar Kebbi.

“Idris ya yi alkawarin cewa gwamnatinsa ba za ta lamunci duk wani abu da ke bata tarbiyya da mutuncin mutanen jihar ba.”

Sakataren ya ce gwamnan ya gargadi dukkan jami’an jihar da su guji yin irin wadannan rubuce-rubuce na rashin kunya a shafukansu na sada zumunta da sauran wuraren taron jama’a.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here