Borno: Zulum ya hana sana’ar gwangwan

0
208

Gwamanan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya hana sana’ar gwangwan a faɗin ƙananan hukumomin jihar 27.

Farfesa Zulum ya ce ya hana gwangwan ne saboda kare masu sana’ar daga mayaƙan Boko Haram da kuma kare dukiyar  da ɓata gari ke sacewa.

Ya ce, “Cikin shekaru biyar da suka gabata ƴan Boko Haram na yawan kashe ƴan gwangwan da suka je neman ƙarafa a ƙananan hukumomin da ke karkara.

“Kuma kun ga kayan da aka kama daga wurin ƴan  gwangwan daga kadarorin gwamnati sai na kamfanonin sadarwa.”

Gwamnan ya ce sakamakon haka ya hana nemo kayan gwangwan, tattara su, safararsu, da kuma cinikinsu a faɗin jihar Borno baki ɗaya.

Kuma ya yi gargaɗin cewa gwamnati za ta haɗa kai da jami’an tsaro wurin hukunta duk waɗanda aka samu na ci gaba da sana’ar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here