Tinubu ya dawo Abuja bayan kwana 2 a Guinea Bissau

0
141

Da yammacin yau Litinin ne shugaba Bola Tinubu ya dawo Abuja daga birnin Bissau, babban birnin kasar Guinea-Bissau, inda ya halarci taron shugabannin kasashe da gwamnatocin kasashen yammacin Afirka karo na 63 wanda aka gudanar a ranar Lahadin da ta gabata.

Jirgin NAF 001 Boeing 737 wanda ke dauke da Tinubu da tawagarsa, ya sauka a filin jirgin saman Nnamdi Azikwe, Abuja da misalin karfe 06:30 na yamma agogon Nijeriya.

Daga nan aka kai shi gidansa na Maitama.

Shugaban na Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya zama sabon shugaban kungiyar ECOWAS ta hanyar amincewa da sauran shugabannin suka yi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here