Mun samu gawar mutum 15, shanu 2,000 sun bace da kuma kone mana gidaje 78 a jihar Filato – MACBAN

0
207

Kungiyar Makiyaya ta Miyetti Allah ta Nijeriya (MACBAN) a ranar Lahadi ta ce an kashe mutane 15 bayan wani farmaki da ake zargin kai musu a karamar hukumar Mangu ta jihar Filato.

Kungiyar ta kuma ce an kona gidaje 78 na mambobinta yayin da sama da shanu 2,000 suka bace bayan farmakin.

Nuru Abdullahi, shugaban kungiyar na jihar ne ya bayyana hakan ga manema labarai jiya, a Jos, babban birnin jihar.

Daily Trust ta ruwaito cewa a ranar Asabar din da ta gabata kungiyar ta zargi ‘Operation Rainbow’, jami’an tsaron jihar da kai wa yankinsu hari tare da kunna musu wuta, zargin da rundunar ta musanta.

Ya ce, “A harin da aka kai a kauyukan Mangu, mun gano gawarwaki 15 da aka kashe a ranar Juma’a. Kimanin gidaje 78 ne suka kone. Shanu da adadinsu ya kai 2,000 har yanzu ba a gansu ba. Wannan abin takaicin ne a jihar.”

Abdullahi ya kuma yi zargin wani shiri na kai wa al’ummarsu hari da wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne.

“Akwai rahoton sirri da ke nuna cewa akwai kwararrun ‘yan bindiga da aka dauka aka kawo su yaki tare da fatattakar duk Fulani daga jihar Filato da sunan rikici. Don haka a halin yanzu muna kira ga gwamnatin tarayya da ta gaggauta kawo karshen abin da ke faruwa a karamar hukumar Mangu.

“Ya kamata su dauki matakin gaggawa kafin al’amura su wuce gona da iri. Muna rokon Gwamnatin tarayya da ta dauki matakin da ya dace don kada al’amura su fita daga hannunsu. Ba za mu ci gaba da kallon yadda mutane ke kashe mu da lalata mana dukiyoyi ba,” Abdullahi ya kara da cewa.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Alabo Alfred, da na runduna ta uku ta rundunar sojojin Nijeriya, Rukuba Barrack, Laftanar Kanar Ishaku Sabastine Takwa, har yanzu ba su amsa kira da sakon da wakilin na Trust ya yi musi kan lamarin ba har zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto.

An samu rikici a kauyukan karamar hukumar Mangu inda aka tabbatar da mutuwar mutane sama da 200 da suka hada da mata da kananan yara a watannin baya.

A halin da ake ciki gwamnan jihar Filato Caleb Mutfwang ya sanya dokar hana fita ta sa’o’i 24 a karamar hukumar Mangu don saisaita al’amura dakile asarar rayuka da dukiyoyi a yankin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here