Za’a samu daukewar wutar lantarki na kwana biyu – KEDCO

0
203

Ma’aikatar rarraba wutar lantarki KEDCO ta sanar da za’a samu daukewar wuta na akalla kwana biyu domin yin wasu gyare-gyare.

Sanarwar ta kunshi sako kamar haka;

“Muna sanar da abokan huldar mu cewa za a samu katsewar wutar lantarki a layin layin dogo mai karfin 330KV Kaduna/Kano a yau Asabar 8 da gobe Lahadi 9 ga watan Yuli 2023.

Kashewar shine don bada damar wasu gyare gyare don inganta aikin wutar na yau da kullum.

Muna ba ku tabbacin cewa TCN za ta dawo da rarraba wutar da zarar an gama aikin.

Muna baku hakuri bisa rashin jin dadi.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here