Sabon harin Sudan ya kashe mutum 22 a birnin Khartoum

0
125

Wani hari da rundunar sojan Sudan ta kai ta sama a birnin Khartoum ya kashe aƙalla mutum 22 tare da jikkata wasu da dama, a cewar wani shaida. 

Mata da yara na cikin waɗanda lamarin ya ritsa da su, kamar yadda waɗanda suka shaida lamarin suka bayyana wa BBC

Harin ya sauka a kan gundumar Dar es Salaam da ke tsallaken Kogin Nilu ta ɓangaren Khartoum a yau Asabar. 

Rundunar RSF da sojojin ƙasar sun shafe aƙalla wata biyu suna yaƙar juna tun daga watan Afrilu. 

Wata majiya daga ma’aikatar lafiya da kamfanin labarai na Reuters ya ambato ta ce mutum 22 ne suka mutu, yayin da RSF ke cewa sun kai 31. 

Yaƙin ya ɓarke ne bayan shugaban sojojin ƙasar, Janar Abdel Fattah al-Burhan, da kuma shugaban Rapid Support Forces (RSF), sun samu saɓani game da makomar ƙasar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here