Majalisar dattawa ta soki gwamnatin Buhari kan jinginar da tashoshin jiragen sama

0
166

Majalisar Dattawa ta soki gwamnatin shugaba Muhammdu Buhari bisa jinginar da tashoshin jiragen sama na Abuja da Kano.

Wannan ya biyo bayan Æ™udirin da Sanatan  Kano ta Kudu, Abdulrahman Kawu Sumaila ya gabatar a zauren majalisar ranar Alhamis.

Ƴan kwanaki kafin cikar wa’adin Gwamnatin Buhari ne dai aka jinginar da tashar jiragen sama ta Nnamdi Azikiwe dake Abuja da ta Malam Aminu Kano dake Kano.

A lokacin ma’aikatar sufurin jiragen sama ta ce jinginar da tashoshin zai samar wa da gwamnati kuɗin shiga da ya zarta $4 biliyan.

Kuma hakan zai taimakawa Najeriya wurin inganta harkokin sufuri.

Sai dai Sanata Kawu Sumaila ya ce an jinginar da tashoshin ne cikin gaggawa ba tare da bin ƙa’ida.

Don haka ya buƙaci gwamnatin tarayya ta soke yarjejeniyar domin bada da duk masu ruwa da tsaki su shiga ayi da su.

Haka kuma ya buƙaci Majalisar ta sa kwamitinta na sufurin jiragen sama ya binciki yadda aka jinginar da duk wata tashar jiragen sama.

Majalisar Dattawan ta amince da wannan ƙudirin nan take.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here