INEC ta maka kwamishinanta Hudu Ari a Kotu

0
172

Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta ce ta maka dakataccen Kwamishinanta na Jihar Adamawa, Barista Hudu Yunusa Ari, a gaban Babban Kotun Jihar.

Hukumar ta ce ta gurfanar da shi ne kan tuhume-tuhume guda shida da suka danganci yin ba daidai ba a zaben Gwamnan Jihar na watan Maris din da ya gabata.

Ana dai tuhumar Hudu ne da bayyana Aisha Binani ta jam’iyyar APC a matsayin wacce ta lashe zaben Gwamnan Jihar, alhalin ba a kammala tattara sakamako ba, kuma ma ba shi ne wanda ya kamata ya bayyana shi ba.

Kwamishinan hukumar mai kula da wayar da kan masu zabe, Barista Festus Okoye ne ya tabbatar da hakan ranar Alhamis a Abuja.

Ya ce INEC ta gudanar da taronta na mako-mako ranar Alhamis, 6 ga watan Yuli, inda ta duba batutuwan da suka shafi gurfanar da wadanda suka aikata laifukan zabe a gaban kuliya.

Festus ya ce a taron da hukumar ta yi da Kwamishinonta ranar Talata, ta tabbatar da karbar korafe-korafe daga ’yan sanda bayan kammala bincike kan laifukan zabe, ciki har da na Hudun.

Shugaban INEC, Farfesa Mahmud Yakubu dai ya sha ba ’yan Najeriya tabbacin gaggauta daukar mataki a kan batun.

Ya ce bayan gurfanar da Hudun, kotun ta sanya ranar Laraba, 12 ga watan Yulin 2023 domin fara sauraron karar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here